Sheikh Jafar Mahmoud Adam - Lakcoci Guda 13 icon

Sheikh Jafar Mahmoud Adam - Lakcoci Guda 13

★★★★★
★★★★★
(4.57/5)

3.3Free2 years ago

Download Sheikh Jafar Mahmoud Adam - Lakcoci Guda 13 APK latest version Free for Android

Version 3.3
Update
Size 92.52 MB (97,011,718 bytes)
Developer first-rate-apps
Category Apps, Lifestyle
Package Name com.andromo.dev658544.app673735
OS 4.1 and up

Sheikh Jafar Mahmoud Adam - Lakcoci Guda 13 APPLICATION description

Wannan app yana dauke da manyan lectures na Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam
Assalamu Alaikum warahmatullah

Wannan app yana dauke da lectures na Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam

wasu daga cikin Lectures din da suke app sune kamar haka:
- Hakkin Iyaye da Na 'ya'ya - Sheikh Jafar
- Hakkokin Mace A Musulunci - Sheikh Ja'afar
-Hukuncin Kida da Waka - Sheikh Ja'afar
-Ciniki Mai Riba - Sheikh Ja'afar
-Kasuwanci Da Amana - Sheikh Ja'afar
- Hukunce Hukuncen Azumi - Sheikh Ja'afar
-Muhimmancin Tarbiya - Sheikh Ja'afar
-Mafiya Mahimmacin Matsalolin Haji Da Umra
-Siffofin Muminai - Sheikh Jafar
-Siffofin Munafukai - Sheikh Jafar
-Tafarki Madai Daici - Sheikh Ja'afar

Allah ya sakawa Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam ya kuma jikansa

Tarihin Sheikh Jafar Mahmud Adam

An haifi marigayi SheikhJa'afar Mahmoud Adam agarin Daura, a shekara ta 1962
(ko da yake wani lokacin yakan ce 1964). Marigayi Sheikh Ja'afar ya fara karatunsa na allo a gidansu, awurin mijin yayarsa, Malam Haruna, wanda kuma dan uwansu ne na jini. Daga nan kuma sai aka mayar da shi wajen wani Malam Umaru a wani gari wai shi Koza, kimanin kilomita 9 a arewa da Daura, wanda shi ma akwai dangantaka ta jini a tsakanin
su, wanda kuma shi nemu sabbabin zuwansa Kano. Bayan sun zo Kano ne tare da wannan malami nasa, a shekara ta 1971 (ko 1972), sai suka zauna a makarantar Malam Abdullahi, wanda asalinsa mutumin jamhuriyar Nijar ne, amma yake zaune a unguwar Fagge a Kano.
Tunkafin zuwansu Kano, tuni marigayi Sheikh Ja'afar ya riga ya fara haddar Alkur'ani mai girma, wanda ya kammala a shekara ta 1978. Bayan da Malam ya kammala haddar Alkur'ani mai girma, kasancewarsa mai sha'awar ilimi, sai ya shiga makarantu biyu a lokaci daya a shekara ta 1980. Ya shiga makarantar koyon Larabci ta mutanen kasar Misra a cibiyar yada al'adun kasar Misra, (Egyptian Cultural Centre), sannan kuma ya shiga makarantar manya da ba su yi boko ba ta Masallaci Adult Evening Classes, tunda a lokacin shekarunsa sun wuce shekaru na primary, amma duk da haka a wannan lokaci shi ne mafi kankanta a ajinsu. Ya kammala wadannan makarantu a shekara ta 1983. Wannan kuma shi ya ba shi damar shiga makarantar GATC Gwale a shekara ta 1984, kuma ya kammala a shekara ta 1988. A shekara ta 1989, malam ya sami gurbin karatu a jami'ar musulunci ta Madinah, a inda ya karanta ilimin tafsiri da Ulumul Kur'an, wanda kuma ya kammala a shekara ta 1993. Sannan kuma Sheikh Ja’afar ya sami damar kammala karatunsa na digiri na biyu (Masters) a Jami’ar Musulunci, A Oundurman Sudan. Sannan kuma, kafin rasuwarsa, ya riga ya yi nisa wajen karatunsa na digiri na uku, wato digiri da digirgir (PhD), a Jami’ar Usman Dan Fodiyo da take Sokoto. Daga cikin malamansa na ilimi, akwai malaminsa na
farko, mutumin kasar Masar, Sheikh Abdul-Aziz Ali al-Mustafa, da kuma Malam Nuhu a unguwar Dandago, wanda malam ya karanci ilimi fikihun malikiyya da wadansu littattafai na hadisi a gurinsa, da kuma Malam Muhammad Shehu, mutumin Lokoja, Akwai kuma Sheikh Abubakar Jibrin limamin masallacin Juma'a na BUK, akwai kuma Dr. Ahmad Muhammad Ibrahim shi ma na jami'ar Bayero ta Kano. Daga cikin karatuttukan da malam ya karantar dasu, sun hada da tafsirin Alkur'ani mai girma, Kitabuttauhiid, Umdatul Ahkaam, Arba'una Hadiith, Kashfusshubuhaat, Bulugul Maraam, Riyaadussalihiin, Siiratun Nabawiy, Ahkaamul Janaa'iz, Siffatus Salaatun Nabiiy. Kafin rasuwarsa, malam ya fara gagarumin aikin rubuce tafsirinsa a harshen Hausa a karkashin cibiyar (Sheikh Ja'afar Islamic Documentation Centre). Marigayi Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam ya rasu ranar juma'a 26/Rabii'u Awwal/1428 (13/04/2007) sakamakon harin da wadansu 'yan ta'adda suka kai masa, a daidai lokacin da yake jagorantar sallar asuba a masallacin Juma'a na Dorayi. Ya rasu ya bar mata biyu, da 'yaya shida, yayin da aka haifa masa ta bakwai kwanaki 58 daidai bayan aiwatar da wannan kisan gilla a kansa. Dubun-dubatar mutane ne daga ko'ina cikin kasar nan suka halarci jana'izarsa.
Allah ya ji kan sa ya gafarta masa, ya saka masa da gidan aljanna.
↓ Read more
Sheikh Jafar Mahmoud Adam - Lakcoci Guda 13 screen 1 Sheikh Jafar Mahmoud Adam - Lakcoci Guda 13 screen 2 Sheikh Jafar Mahmoud Adam - Lakcoci Guda 13 screen 3 Sheikh Jafar Mahmoud Adam - Lakcoci Guda 13 screen 4 Sheikh Jafar Mahmoud Adam - Lakcoci Guda 13 screen 5 Sheikh Jafar Mahmoud Adam - Lakcoci Guda 13 screen 6

Old versions

Version Size Update
⇢ 2.1 (1 variants) ↓ 92.76 MB ◴ 5 years ago
⇢ 1.0 (1 variants) ↓ 92.71 MB ◴ 6 years ago
⇢ 3.3 (2 variants) ↓ 92.52 MB ◴ 2 years ago